Ad Code

Latest Post

Mulki ƴan Hadejia: Nazarin tufka da warwara game da son kan yankuna a Jihar Jigawa


 Mulki ƴan Hadejia: Nazarin tufka da warwara game da son kan yankuna a Jihar Jigawa


Gabatarwa:

"Jigawa tarin Allah" kamar yadda ake mata take ko laƙabi, Jigawa jiha ce ta mutane ɗaya masu al'adu iri ɗaya harma da addini da sauran abubuwa na more rayuwa wanda suka haɗa yanki na Hadejia, Dutse, Gumel, Kazaure da Ringim. Rashin bambancin da ake da shi na rayuwa wata ni'ima ce da Allah maɗaukakin Sarki ya yiwa jihar ba kamar sauran jihohin dake Najeriya ba. Saboda haka, Shi ya cancanci yabo ba kowa ba.

Mulki a jihar Jigawa:

A taƙaice, jihar Jigawa ta samu matuƙar cigaba ta dalilin wakilan shugabannin da take samu tun daga kafata a 1991 zuwa wannan shekarar. Jihar Jigawa tayi shugabanni na soja da farar hula wasu ma daga yankuna mabanbanta na jihar kawo zuwa wannan lokaci. Kowanne shugaban a lokacin da yayi mulki yayi daidai gwargwadon kwazonsa domin cigaban jihar. A dalilin haka, duk ƴan Jigawa suna alfahari da kowanne shugaba da yayi mulki jiya ko yake yi yau harma da wanda zai yi gobe.

Mulkin siyasa a jihar Jigawa a tarihi ta ɓangaren shiyya (senatorial districts) ya fara samuwa inda mutum 2 suka yi mulki daga shiyya ta tsakiya, haka zalika, mutum 2 suka yi daga shiyya ta Arewa sannan babu wanda yayi daga shiyya ta gabas. A rabe-raben masarautu da ake dasu guda biyar; Dutse tayi sau uku, Kazaure biyu, Ringim ma ta yi biyu, Gumel da Hadejia ba suyi ko ɗaya ba.

Game da mulkin masarautar Hadejia da shiyyar Jigawa ta gabas:

A dawowar siyasar jihar Jigawa (1999-2022), yankin Hadejia yafi kowanne yanki a jihar Jigawa samun albarka ta rike muƙamin mataimakin gwamna wanda aka yi har sau biyar, inda yankin Gumel suka riƙe sau ɗaya daga bisani Hadejia ta ƙarasa a shekarar 2015 ya zama shida. Alƙalami ya nuna sunfi kowa samun madafin iko na juya jihar Jigawa a kowanne fanni na jihar Jigawa; kama daga fannin ilimi, lafiya, ma'aikatu da wasu guraren mabanbanta.

Bayan jihar Jigawa, a tarayyar Nigeriya da sauran ƙasashen waje Hadejia ta yi ƙaurin suna wajen samun gogaggun mutane da ake fafatawa da su a kowanne fanni na rayuwa. An gano cewa wasu da yawa daga jihar Jigawa idan sun fita da sunan Hadejia suke amfani da alfahari koda su ba yan yankin ba ne. Zamu ce zama yayi daɗi kenan.

A taƙaice, batun manya ta fannin boko da tattalin arziki da wasu manyan abubuwan da suka bayyana, harda girman gari da sauransu babu inda ya kai yankin Hadejia a duk yankuna dake fadin jihar Jigawa. Duk wani sashe na mulkin jihar Jigawa babu abinda yankin bai taba samu ba sai riƙe muƙamin gwamna – wanda shike jan ragamar al'amurran gudanarwa na jiha gaba ɗaya.

Nazari akan rabuwar kan masarautun jihar Jigawa:

A yanayin mu'amala ta Sarakunan masarautu guda biyar da ake da su a jihar Jigawa babu wani abu daya fito fili wanda yake nuna bangarenci a tsakanin su. Haka zalika, masu kasuwanci da neman ilimi da zumunci na aure suna shiga kowanne yanki domin yin mu'amala mai kyau, babu wani tushen zancen bin ƙwaƙƙwafin asalin ƙaramar hukuma balle masarauta ko shiyya.

Ta wani ɓangaren, wayayyun ƴan siyasa suna huɗɗa mai tsafta tsakanin su, daga kowacce shiyya ko masarauta ba tare da nuna wani abu dake nuna bambancin wajen zama a tsakanin su ba, koda ba ra'ayi ɗaya ko jam'iyya ɗaya akeyi ba. Masu wayon har furtawa suke suce 'siyasa bada gaba ba'. Ansha samun wanda suke samawa wasu aiki daga yankin da ba nasu ba, ko suyi zumunci da kyautatawa ga wanda ba ɗan masarautar su ba - kuma ko tashin zance ba'a yi. A taƙaice dai kyawawan abubuwan da suka bayyana sunfi yawa a tsakanin masarautu na jihar Jigawa.

Saboda haka, zancen bangarenci ko sonkai wani abu ne da wasu suka ƙirƙira domin cimma wasu manufarsu, ta hanyar jefa kiyayya tsakanin yankunan gaba ɗaya. An kirkiri hakan zuwa ga talakawa wadda daga baya zata zo ta shafi masu jagorantar su.

Wanna matsalar yanzu haka ta samu dama har ta shigo abubuwa na siyasa. Ta kuma fara mamayar talakawa da masu ruwa da tsaki akan jagorancin jihar. A zahiri amma, ba a cika samun irin wannan matsala ta sonkai ko ɓangarenci ba a mu'amala ta yau da gobe. Kusan abu ne da ake yawo da shi a baki wadda ya raba kawunan mutane shekaru masu yawa da suka wuce zuwa yanzu.

Ƙalubalen da jihar Jigawa take/zata fuskanta:

Al'amura sun fara fitowa wanda suka bayyana cewa anada matsalar rashin haɗin kai na mutanen yankunan dake faɗin jihar Jigawa wanda ake kallon cewa na yankin Hadejia ne ya fito fili a. A gaskiya anci galabar wasu yan Hadejia ne wajen nuna musu cewa sauran yankunan jihar Jigawa basa sonsu. Hakan ne yasa sauran yankunan suke tunanin yan Hadejia sun fara fifita kansu akan sauran bangarorin. Daɗi-da-ƙari, idan suka samu damar hayewa sama da kowa baza suyi musu adalci ba. Wannan fa duk tunani ne ba wai ta tabbata ba ne.

Duk da akwai wanda suke amfani da wannan damar ta rarrabuwar kai a jihar Jigawa domin cimma wasu manufofin su, to idan shugabanni suka bari tayi nisa to zaman lafiya zai fara rushewa, tattalin arziki zaiyi ƙasa, zumunci zai yanke da wasu dubban ni'imomi da ake morewa tare a matsayin jiha ɗaya. Idan aka rabu, to ina muka dosa? Wannan tunanin kowa ya kamata yayi.

Tsokaci akan siyasar Hadejia:

Kusan sanin kowane cewa siyasa a Najeriya ana fara tane daga jam'iyya, inda waƴanda suka daɗe suna mata hidima daga karshe suke zama wanda suke juyata da kula da al'amuran dake cikin ta. A yanzu dai babu wani jagora ko shugaban na wata jam'iyya a yankin Hadejia. Yan yankin Hadejia ya kamata suna jurewa wajen zama a cikin jam'iyyar da suke da ra'ayi kuma suke tunanin zata musu rana, wata kila har sa mallake ta sannan su samu ragamar amfani da ita ta yadda suke buƙata.

Haka zalika, matasan yankin su zama masu juriya da haƙuri wajen bin shugabannin su domin cigaba da dore kyawawan abubuwan da suka gabatar a baya. Faɗa da manya babu abinda yake samarwa sai dana-sani da rashin nasara idan ba a kan gaskiya akayi ba.

Yan takarar a kusan kowacce jam'iyya za'a iya samun fiye da ɗaya ko biyu. Shin me ya kamata ayi domin haɗa kansu a gida su janyewa wanda ya cancanta da kuma umarnin bin wanda aka sahalewa? Hakan ina tunanin zaifi bawa kowa dama ya mora cikin kwanciyar hankali.

Ya kamata a sami ƙungiyoyin manya su yawaita wanda za ana raba ƙafa dasu wajen tuntuɓar shugabanni da wayar da kan al'umma akan abinda ya shafi siyasa. Da yawan talakawa basu san abubuwan da yake faruwa na gaskiya ba, sai tunanin da aka cusa musu na son wane da ƙin wane. Ashe kuwa, ƙungiya ɗaya ko biyu tayi kaɗan akan wannan jan aikin. Ta hanyar hakan ne zasu dakatar da wanda suke cin mutuncin mutane a bayyane, wanda ya ke nuna rashin haɗin kai tun a gida kuma son rashin zaman lafiya ga sauran yankunan jihar babi ɗaya.

Akan wannan batu, ya kamata a bawa Hadejia dama domin tabbatar da kwarewar ta daga cikin yayan da take da su. Ko ince, ya kamata Hadejia ta fito ta nema domin nuna soyayyar ta ga jihar Jigawa da kuma ƙaryata zargin da ake mata na ɓangarenci a jihar. Na tabbatar da cewa Hadejia ta cancanta kuma tanada wayanda za suyi mata wakilci mai kyau.

Shugabanci a zamanance:

A shugabanci na zamani (21st century leadership) ana neman jajirtacce wanda yake da ƙwarewa ta iya mulki wanda zai kawo wa kowacce ƙasa ko jiha ko ƙaramar hukuma cigaba ta fannin ilimi, tattalin arziki, zaman lafiya da sauransu. Ba'a hana amfani da yanki ko wani ma'auni na tantancewa ba, amma da za a bi cancanta ta gogewa (experiences) da ilimin (knowledge) da hakan sai yafi kawo cigaba. Kada a bari tasirin abubuwan da suka faru kusan shekaru talatin yayi tasirin a wajen durkushe wata jiha ko yanki. Yanayi yana canjawa salo yana canjawa.

Ina mufita ga rarrabuwar kan jihar Jigawa?

A ji tsoron Allah; ya kamata a dena amfani da tunanin masu hankalin cikin mu wajen cin moriyar wasu tsirarun mutane na karamin lokaci. Duk waƴanda suka gyara, to sun gyara harda ƴaƴansu da jikokin sa. Kuma idan suka gurɓata to lalata al'ummar gaba daya suka yi. Wasu tsoron shiga wannan rukunin ne yasa suke komawa baya. Ya kamata a ƙarfafe su indai akwai gudummawar da zasu iya bayar wa.

Ya kamata ana cire son mutum daya ko biyu (interest) ana duba bukata na al'umma da kuma inda suka karkata domin tafiya tare bai ɗaya. Ma'ana, a gudu tare a tsira tare.

A matsayin mu na yan zamani da al'amura soka zo mana da sauki ta hanyar ilimi da ya samu — koda dai bai wadata ba. Ya kamata wanda suke da ilimin suyi binciken hanyar da za'a kara hoɓɓasa danganta mai karfi tsakanin masarautu da shiyyoyin jihar Jigawa.

Shawara:

Talakawa ya kamata suyi karatun ta nutsu, kan cewa ba koda yaushe ne ɗan garin ka ko yankin ka ke maka rana ba idan bai san yadda ake yi ba ko bai iya ba. Faɗa ko wucewa gaba don saboda yanki, yare ko addini baida wani amfani a siyasar Najeriya. Da so yana aiki da yanzu Arewacin Najeriya ya zama daular Larabawa. Akan haka, idan kayi faɗa da ɗan uwanka to an barku da jin kunya da asara, domin mafi yawa na kason shugabanni manya da yan kasuwa da yan boko kansu a haɗe yake.

To sum up, "leadership" is a complex, complicated and difficult phenomenon; who're in the system know better only. So, don't conspire against anybody, what goes around, comes around.

Kammalawa:

A ƙarshe, ya kamata mu tuna ɗaya daga cikin wanda Allah ke darajawa shine wanda yafi amfanar al'ummar sa, sannan Shi ke bada mulki a lokacin da yaso kuma ga wanda ya so.

Yin ƙwazon neman da kuma addu'a yafi dacewa wajen neman kowacce irin bukata. Haka zalika, Hausawa suna cewa, 'wani hanin ga Allah baiwa ne', sannan 'zama lafiya yafi zaman ɗan sarki'. Kuma kowa ya sani soyayya rahama ce sannan ƙiyayya wuta ce. Allah ya hada kan yan Jigawa da shugabanin mu gaba ɗaya Ya kuma bamu shugabaci na gari, amin.

Amir Muhammad Harbo,
16 ga Maris, 2022.

Post a Comment

0 Comments