Mu yi hulɗa da kowa daidai da hankalinsa.
Akwai wayanda suna da shekaru amma hankalin ba mai gamsarwa ba ne. Haka zalika, akwai masu hankali a cikin mutane masu ƙanƙantar shekaru. Saidai amfi samun masu shekaru da cikekken hankali.
Akwai wani wani labari da wata rana naci karo da shi tsakanin wani yaro da ubangidansa. Wani yaro ne mai wauta ubangidansa yake aikensa gida domin ya kai masa kayan amfani a gida. Watarana ya aike shi da leda cike da kayan marmari yakaiwa matarsa, sai ya tarar ba kowa, ya dawo ya kawo masa kayansa. Kawai sai maigidansa yai wuf ya ce, ai kuwa da jefawa ka yi ta kan katanga idan sun dawo sai su gan shi su ɗauka suyi amfani da shi. Amma yanzu dole sai kasha wahalar komawa idan sun dawo.
Wata rana sai mai gidan ya kira yaron ya sake bashi leda dauke da wani abun a ciki. Yaron nan ya sake zuwa gidan da wannan ledar da maigidan ya aike shi amma bai tarar da kowa ba. Nan take sai ya yi aiki da waccan shawarar ta farko da mai gidansa ya bashi, kawai sai ya wurga ledar ta saman katanga.
Ko kunsan mene ne a wannan ledar a wannan aiken da yayi masa? To ƙwai ne. Sabo da haka, mu yi hulɗa da kowa daidai da hankalinsa. Allah Ka bamu nutsuwa ta kyakkyawan hankali; amin.
0 Comments