Ad Code

Latest Post

Muhimmanci ko falalar yin addu'a ga Musulmi


 Muhimmanci ko falalar yin addu'a ga Musulmi


-Bismillahir Rahmanir Raheem

Tsira, salati da amincin Allah su tabbata ga zababben Allah, shugabanmu Annabi Muhammadu SAW, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa amintattu.

Sanannen abu ne cewa kowanne irin bawa yana kusantar Ubangijin sa, Allah (SWT) ta hayoyin ibada daban-daban kamar Sallah, Azumi har da addu’a a karan kanta. Mutum yakan yi addu'a a duk lokacin da ya samu dama cikin dare ko yini, a lokacin farin ciki, kunci ko tashin hankali, da sauransu.

Allah SWT ya kasance mai karban addu’ar bawansa a kowanne yanayi da lokaci, idan bawan ya rokeshi, ya maida al’amarinsa agareshi kuma ya tabbatu cewa ya dogara agareshi.

Akwai ayoyi daban-daban da sukayi bayani game da addu'a ko roko ga Allah SWT a cikin Alkur'ani Mai girma. Ɗaya daga cikinsu itace ta cikin suratul-Bakara: “Idan bayina suka tambaye ka inda nike, ka ce musu ina kusa, kuma ina amsa addu’ar mai addu’a idan ya roke ni…”

Falalar yin addu'a:

Addu'a tana da girma, daraja, martaba da girman sha'ani ga wadda ya jure yake yinta dare da rana a bisa tsari wanda Allah da ManzonSa (SAW) sukayi bayanin yadda za'ayi.

Saboda falalar Addu'a Ubangiji mai Girma da daukaka yake cewa a cikin Suratul Gafir aya ta (60). "Ku rokeNi, sai na amsa muku wadanda sukai girman kai, ga barin bauta a gareni zan shigar dasu wutar Jahannama", kaga ashe duk wadda baya addu'a ko kuma yana shakku akanta to yana daga masu girman kai.

A taƙaice, falalar yin addu'a a garemu itace hanyar da Allah yake biyawa bayinsa bukatu duk yawansu.

Abubuwan da ya kamata mu fahimta:

Manzon Allah SAW yace : "Hakika Allah Madaukakin Sarki rayayye ne, kuma mai karamci ne. Yana jin kunyar mutum ya cira hannyensa gareShi, kuma ace ya dawo dasu taɓaɓɓu babu komai akansu" (Sahihul Jaami'i).

Kun ga wannan hadisin yana karantar damu cewa mu rika kyautata tsamaninnu ga Ubangijinmu. Lallai shi yana jin kunyar mu rokeshi bai amsa mana ba.

Ya kamata muna kyautata lafazi acikin duk abinda zanu roki Allah (SWT) domin samun biyan buƙatar mu.

Bayan haka, mu dena cewa mun yi addu'a ba a karba ba, domin Yakan ma amfani da addu'ar da muka yi ta inda zata fi mana amfani ne. Ma'ana, muna kyautata tsammani ne zuwa ga Ubangijinmu. Sannan mu dena yin mummunar addu'a ko tsinuwa ga mutane.

Sirrin dake cikin amsa addua a takaice:
Na farko: Tsammani. Na biyu: Hakuri ko rashin gaggawa. Na uku: Juriya. Na huɗu: Yi akan abu mai kyau.

Hakika Allah (SWT) ya na karbar addu’a a wajen bawansa, kuma yana jinsa, yana sane da halin da yake ciki. Babban muhimmin al’amari shi ne bawa ya tsare dokokin yi da karban addu’a kuma ya dage da addu’ar domin bata faduwa kasa banza. Bawa ya yi addu’ar sa cikin kowane yare, ako wane lokaci, cikin tsananin imani da Allah da yarda da cewa Allah zai karbi wannan addu’ar tasa a lokacin da tafi muhimmanci.

Ubangiji Allah (SWT) ya biyawa kowa bukatunsa na alheri, amin.

Post a Comment

0 Comments