Ad Code

Latest Post

Tsokaci Game da Ranar Hausa

Ba zamu ciyar da Harshen Hausa gaba yadda muke zato ba, muddin muna watsi da al'adar yaren ta hanyar rungumar wasu abubuwan da ba nashi ba muna maye gurbin su da baƙi waɗanda suka ci karo da shi ta fuskar al'ada.


Saboda haka, dole mu dawo da kishin sa ta hanyar amfani da al'adar sa; sanya tufafin Hausawan, da cin ire-iren cin abincin su da sauran abubuwa na rayuwa cikin harda shagulgulan wasa da biki da tarurruka mabanbanta. Hakan bazai kore ƙirƙira ko samar da wasu abubuwa sabbi a cikin harshen idan babu su ba.

Ina ganin zai taimaka wajen ciyar da harshen Hausa gaba da al'adar Hausawa. Allah ya taimake mu gaba ɗaya, Ya cika mana burin mu mai kyau, amin. 
Kullum ina samun kaina cikin farin ciki ganin yadda kimiyya da fasaha ke sake ƙarbar yaren Hausa wajen gudanarwa ba a iya nahiyar Afirka ba harma da ƙasashen Turai da Asiya.

Ya zama wani nauyi wajen mu da mu sake inganta shi ta hanyar sabbin bincike, rubutu, yin waƙoƙin, kai harma a yayin kasuwancin mu da sauransu.

Haka zalika, a wannan lokacin ya kamata ƴan jarida su ƙara ƙwazo wajen amfani da ƙa'idojin sa wajen yin rahotanni da labarai a kafafen su mabanbanta domin tabbatar da daidaitacciyar Hausar Boko da ya kamata kowa zaina amfani da ita. A zahiri sune fuskar da ake kalla a wannan yanayi na kafafen sadarwa a yanke mana hukunci mai kyau ko akasin haka.

Godiya ta tabbata ga Ubangiji mamallakin kowa da komai cikin harda harshen Hausar. Muna addu'ar Allah ya sake bamu haɗin kai da dukkan yaren da suke duniya baƙi ɗaya ya bamu zaman lafiya, amin.

Ina mana barka da taya murna da zagayowar wannan Rana ta Yaren Hausa. Fatan alheri!
#Ranar_Hausa

Post a Comment

0 Comments