AREWAR MU?
Abinda ke zuciya zan bayyana.
Koda ace baza mu rayu ba.
zama a Arewa kamar ba zai yuwu ba.
Shin ina wakilan mu da muka zaɓa.
Kariyar ne ba zasu bamu ba?
Kunsan bazan musu ƙage ba.
Sun toshe kunne basu ɗauki komai ba.
Dan su kare dukiyar mu da kowa ba.
Ko ina duhu babu haske, Rabbi mun tuba.
Da suna kishin mu kamar iyalansu.
Uzurin mu da bazasu maidashi kamar ba nasu ba.
Da har abadan baza su gujemu ba.
Arewa ta zama kamar babu kowa,
Mun rarrabu kamar ba yankin Balewa da Sardauna ba.
Waƴanda sukai komai dan a tsira tare ba.
Musan munki ji dole bazamu ƙi gani ba.
Komai ya tashi baruwan su da talaka ba.
Mai wuni a rana dan ya zaɓe su ba.
Ya Rahimu laifin da mukai ba zamu ƙara wani ba.
Ga hawaye a idaniya don wuya.
A yaye mana wannan ukuba.
Amir Harbo,
November 25th, 2020.
0 Comments