Ad Code

Latest Post

Arewa Inane Matsayar Mu?

 Arewa Inane Matsayar Mu?

Duk da munsan cewa mun gama bauta ƙarƙashin turawan mulkin mallaka, akwai wata sabuwar bautar da mukeyi tuntuni ƙarƙashin ƴan kudancin ƙasarnan. Wannan babu ja!

Duk dadai nasan na dauko batu mai girma amma ba ina faɗa bane dan san rarrabuwar kai ko tashin hankali saidai dan musan inane ke mana ciwo kuma mu kawo gyara.

Wannan bautar da muke ƙarƙashin ƴan kudancin ƙasarnan tafi ciwo, wulaƙanci da ƙasƙanci akan ta mulkin mallaka. Abun haushin shine yan Arewan basa kishinta ta kowanne bangare tun daga shuwagabannin ta harda mabiyan ta.

A kullum abunda ke cutar wannan yanki,   shine nuna banbanci na siyasa da kullum yake daƙushe mu. Idan da zamu tuna yadda masu kishin Arewa sukasha wahala da juriya da baza mu manta da Sir Abubakar Tafawa Balewa ba, da Sir Ahmadu Bello da sauransu.

A irin wannan yunƙuri da sukayi na kawowa yankin nan cigaba ba tareda ƙyashi, hassada da Kuma nuna banbanci addini ko bangaranci ba shi yasa kullum muke musu addu'a Allah ya kyautata makwancin su. Allah yasa, Amin.

A ta wannan dalilin ne na kishin Arewa har Sir Ahmadu Bello wasu da haɗin guiwar sojoji ƴan Kudu marasa kishi suka kashe shi a 15/01/1966. Haka aka yiwa Sir Abubakar Tafawa Balewa haka kuma duk wani wanda zaiyi wani yinƙuri na kishin Arewa so suke suga bayansa.

Sir Ahmadu Bello ya tashi tsaye kuma kirkiro abunda ake ce masa "Northernization Policy". A bisa wannan tirbane har aka Samar da Jami'ar Ahmadu Bello dake zariya. 

Tun daga lokacin ne aka fara samun bunkasa ta hanyar ilimi. Amma a yanzu anyi watsi da wannan abunda ya kawo domin a kullum bama kishin kammu.

An kashe mana manyan mu masu kishin mu, an musu ƙarya da ƙage da cewa suna tafe da 'Banbancin Alkarya' da kuma 'Cin hanci da Rashawa'. 

Ance mun fiya cin hanci. Shin ƴan Arewa ne kadai masu cin hancin? Amma yanzu tabbas munga inda ake cin hanci da rashawa wanda har ya wuce munsheran. Misalin NDDC wanda ya faru a kwanannan hujja ne.

Buharin da muke taƙama dashi, karfin guiwar mu ya fara karewa. Saboda baya samu gudunmawar masu kishin yankin. A kullum fargaba nake ya Arewa zata kasance nanda shekaru kaɗan masu zuwa.

Bai kamata mu manta da wannan rana ba (16/01/1966) wanda waƴansu ƙabila suka cuci kasarmu musamman yankin Arewa inda Chukwuma Nzeogwu yake ikirarin cewa sun kifar da gwabnatin Arewa sun huta.

Mun shaida har shagulgula sukayi wanda sukai masa laƙabi da "January victory", Amma mu kuwa gashi ayau muna kuka! Babu masu cetan mu. Sir Abubakar Balewa da Brigadier Zakariyya Maimalari, Umaru Musa Yar'adua, Abba Kyari, Malam Aminu Kano da sauransu sun tafi.

Hakika da wayanda suka biyo bayan wayancan mutanen a siyasar Arewacin kasarnan sun dora daga wajen da suka ajiye da yanxu Arewa ta taka wani mataki na cigaba wanda bazai misaltu ba.

Inda zamu tuna lokacin mulkin Obasanjo duk manyan muƙaman daya bayar na Mutanansu ne, sukuma mutanan sukaiwa ɓangarensu gata, ba tareda da handama ba suka inganta yankin su. Waƴannan abubuwan sun haɗa da power/wuta, suka gyara Industries dinsu, Iimin su da tattalin arzikin su. Amma mu fa?

Inaso wannan rubutun ya zama Allura ta kaimi ga duk wani ɗan Arewa, Bahaushe ko Babarbare ko Bafulatani da duk wani yare, musulmi ko kirista da yasan akwai wani nauyi da yake kansa dan cigaban yankin sa ako ina yake. 

Allah ya taimaki Arewa ya bawa Najeriya Zaman lafiya. Amin.


-Amir Muhammad Harbo

August, 2020.

Post a Comment

0 Comments